Matakan Da Mutanen Kasar Indonasiya Suka Dauka Na Haramta Sayan Kayakin Da Aka Yi  A HKI Ya Yi Tasiri A Kasar

A zanga-zangar da mutanen kasar Indosaniya suke gudanarwa a karshen ko wani mako, don nuna goyon bayansu ga al-ummar falasdinu a Gaza, sun kuma haramta

A zanga-zangar da mutanen kasar Indosaniya suke gudanarwa a karshen ko wani mako, don nuna goyon bayansu ga al-ummar falasdinu a Gaza, sun kuma haramta sayan duk kayakin da aka shigo da su kasar daga HKI, wanna ya haddasa asarori ga kamfanonin haramtacciyar kasar wanda ya kai dalar Amurka biliyon 21.5 a cikin watanni 4 na farko na wannan shekara ta 2024.

Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bayyana cewa, dakatar da sayan kayakin HKI a kasar Indonisiya ya ragu da kasha 60% a kasar idan an kwatanta da lokaci irinsa a shekara ta 2023, kafin a fara yaki a Gaza.

Kamfanonin kasuwanci masu manya manyan shaguna a kasar sun dakatar da sayan kayakin da suke fitowa daga HKI. Daga cikin kamfanonin HKI da suka yi asara a kasar Idonasiya dai, sun hana da MacDonald da kuma Puma.

Kasar Indonasiya dai tana daga cikin kasashe 5 na farko wadanda suka haramta sayan kayakin da aka kera a HKI a kasashensu. Labarin ya kara da cewa maimakon kayakin HKI mutanen kasar suna sayan irin wadannan kayaki na cikin gida ko kuma na kasashen larabawa da musulmi.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments