Shugaban Kasar Tunusiya Ya Jaddada Bukatar Karfafa Matakan Tsaro Kafin Zaben Kasar

Shugaban kasar Tunisiya ya yi kira da a sanya ido sosai kan duk wani yunkuri na neman rura wutar fitina kafin zabe a kasar Shugaban

Shugaban kasar Tunisiya ya yi kira da a sanya ido sosai kan duk wani yunkuri na neman rura wutar fitina kafin zabe a kasar

Shugaban kasar Tunisiya Qais Sa’id ya yi kira da a yi taka tsan-tsan game da duk wani yunkuri na neman ruruta wutar rikici a dukkan yankunan kasar gabanin zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a ranar 6 ga watan Oktoba mai zuwa, bisa la’akari da cewa yunkuri ne da wadanda suka fitar da rai daga  shugabanci kuma dole ne a dakile su.

Wannan ya zo ne a wata ganawa da aka yi tsakanin shugaba Sa’id da ministan cikin gidan kasar Khaled Al-Nuri, a fadar mulkin kasar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: A yayin taron, Sa’id ya yi nazari kan yanayin tsaro a kasar baki daya, inda ya lura da kokarin da jami’an tsaro tare da sojoji suke yi na tabbatar da tsaron kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments