Ministan Harkokin Wajen Iran Ya Jaddada Aniyar Kasarsa Ta Kyautata Hudda Da Kasashen Turai

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ma’aikatarsa a karkashin sabuwar gwamnatin Iran za ta shiga cikin fagen kawar da zaman dar-dar da ke tsakaninta

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ma’aikatarsa a karkashin sabuwar gwamnatin Iran za ta shiga cikin fagen kawar da zaman dar-dar da ke tsakaninta da Amurka da kyautata alaka da kasashen Turai matukar suka daina kiyayya da kasar ta Iran

A hirarsa da kamfanin dillancin labaran Kyodo na kasar Japan game da makomar hadin gwiwa tsakanin Iran da Japan, Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Suna da masaniya kan kwarewar Japan a fagen harkar makamashi, man fetur, da tattalin arziki da irin muhimmiyar rawar da zata taka a kasar Iran.

Ya ci gaba da cewa: Iran da Japan suna da gagarumin karfin da za su iya kulla alaka mai dorewa da cin moriyar juna a duk fadin nahiyar Asiya don ci gaba da bin hanyar haɗin gwiwa mai amfani.

Dangane da batutuwan da sabuwar gwamnati ta sa a gaba wajen gudanar da hadin gwiwa da kasashen gabashin Asiya, Araqchi ya ce: Sabuwar gwamnatin Iran ta tsara babban buri a manufofinta na waje na kulla alaka da kasashen gabashin Asiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments