Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta tabbatar wa kasashen Turai hakkinta na mayar da martani kan haramtacciyar kasar Isra’ila
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Hakki tabbatacce na Jamhuriyar Musulunci ta Iran mayar mayar da martani kan aikin wuce gona da iri da gwamnatin yahudawan sahayoniyya suka aiwatar a birnin Tehran.
A tattaunawa ta hanyar wayar tarho da takwaransa na Faransa Stephane Segorn, Abbas Araqchi ya yi ishara da tarihin alakar da ke tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Faransa, ya kuma jaddada aniyar Iran na inganta tattaunawa mai ma’ana a cikin tsarin fadada hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.
Ya yi nuni da irin sarkakiya da batutuwan da suke faruwa a yankin yammacin Asiya da kuma manufofi da ayyukan yahudawan sahayoniyya da ke da nufin kara tada hankali da fadada fagen rashin zaman lafiya a duk fadin yankin.
Araqchi ya yi kira ga Faransa da sauran bangarorin yammacin duniya da su mayar da hankali kan yahudawan sahayoniyya a matsayinsu na kanwa uwar gami na abin da ke faruwa a halin da ake ciki domin hana fadada yaki da kuma tada zaune tsaye a yankin.