Iran ta ce za ta ci gaba da tallafawa Syria, kasashe masu adawa da siyasar Isra’ila

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da tallafawa kasar Siriya da kuma dukkanin kasashen

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta ci gaba da tallafawa kasar Siriya da kuma dukkanin kasashen da ke goyon bayan gwagwarmayar da suke yi da gwamnatin Isra’ila.

Araghchi ya yi wannan tsokaci ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da ministan harkokin wajen Syria Faisal Mekdad a ranar Juma’a, wanda ya taya babban jami’in diflomasiyyar Iran murna kan sabon aikinsa.

Mekdad ya ce Damascus ta kuduri aniyar inganta huldar abokantaka da Tehran.

Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da na Siriya sun jaddada wajabcin ci gaba da tuntubar juna kan hanyoyin inganta alaka a bangarori daban-daban.

Araghchi da Mekdad sun jaddada muhimmancin tsayawa tsayin daka kan ayyukan wuce gona da iri na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, da kuma goyon bayan Falasdinu.

Ministocin biyu sun gayyaci juna domin kai ziyara Tehran da Damascus.

Har ila yau a wata tattaunawa ta wayar tarho da ministan harkokin wajen kasar Labanon Abdallah Bou Habib a jiya Juma’a, Araghchi ya ce tsarin sabuwar gwamnatin Iran ya ginu ne kan bayar da karin goyon baya ga gwamnatin Lebanon da al’ummar kasar da kuma tsayin daka wajen tunkarar zaluncin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments