Karamin Ministan tsaron, Bello Matawalle, ya ba da umarnin a bi diddigin waɗanda suka kashe Alhaji Isa Bawa, Hakimin Gatawa a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, tare da tabbatar da an gurfanar da su a gaban shari’a.
A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar, Henshaw Ogubike, ya fitar a yau Juma’a, Matawalle ya yi Allah wadai da kisan, yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici da ba za a amince da shi ba.
Ya jaddada cewa ba za a lamunci irin wannan aika-aika ba, sannan ya umarci babban hafsan tsaro da ya gudanar da cikakken bincike don kamo waɗanda suka aikata wannan ta’addanci.
Matawalle ya yi nuni da cewa batun tsaro na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sa a gaba, kuma tana ba Sojojin Najeriya cikakken goyon baya wajen wannan yaki.
Ya tabbatar da cewa Rundunar Sojojin Nijeriya za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin cewa waɗanda suka aikata wannan laifi sun fuskanci hukunci. Ministan ya kuma jajanta wa iyalan marigayi Hakimin, da mutanen Gatawa, da ma gwamnatin Jihar Sakkwato.