Limamin Da Ya Jagoranci Sallar Jumma’a A Nan Tehran Ya Ce Tattakin 40 Na Bana Ya Sha Bamban Da Na Shekurun Baya

Limamin da ya jagorancin sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam Kazim Sadiki ya bayyana cewa tattakin miliyoyin masu ziyarar 40 na Imam Hussain(a) na

Limamin da ya jagorancin sallar Jumma’a a nan Tehran Hujjatul Islam Kazim Sadiki ya bayyana cewa tattakin miliyoyin masu ziyarar 40 na Imam Hussain(a) na wannan shekarar ya bambanta nesa ba kusa ba, da na shekarun da suka gama.

Kamfanin dillancin labaran IRIB-NEWS ya nakalto limamin yana cewa ziyarar 40 na Imam Hussain (a) ga ma’abuta sanin All..ko Arafaa yana da matsayi na musamman. Amma zirar 40 na Imam Hussain (a) a bana ga sauran mutane, ya zama abin alfakhari ga duniyar musulmi, musamman kasar Iran wacce take da babban rabo a shiryawa da kuma gudanar da tattakin 40 zuwa hubbaren Imam Hussain (a) limami na 3 daga cikin liamamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s).

Hujjatul Islam Sadiki ya ce, miliyon Iraniyawa suna ziyartar birnin Karbala madaukaki da ke kudancin kasar Iraki a kwankin 40 na shahadar Imam Hussain (a).

Sannan daga karshen limamin yayi kira ga sabuwar gwamnatin JMI ta Dr. Masoud Pazeshkiyan ta zamanto mai tafiya tare da wiliyul Fakhih a ayyukan gudanar da kasar, saboda samun nasara a abinda ta sa a gaba. Ya kuma kara da cewa, Imam Khumaini (q) wanda ya assasa JMI ya  taba cewa matukar mutane sun sanya waliyul Fakhih a gaba, a kuma cikin harkokin gudanar da kasa, ba zasu taba cutuwa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments