Mambobin kungiyar mawaka da yabo na Muhammad Rasulullahi (s.a.w) na babban birnin Tehran sun halarci titin Arbaeen Husaini (a.s) tare da gabatar da shirin a jerin gwano daban-daban.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kungiyar mawaka da yabo ta Muhammad Rasulullahi (s.a.w) ta halarci ayarin kur’ani na Arbaeen Darul-Naim, domin samar da yanayi na wa’azi a lokutan bukukuwan Arba’in Hosseini na kasar Iraki.
A yayin tattakin na Arba’in ‘yan kungiyar sun gabatar da shirye-shirye da ayyuka na kur’ani tare da rera wakoki da tawasih a cikin jerin gwanon da ke Najaf, hanyar tafiya da Karbala.
Mambobin wannan kungiya da a kowace shekara suke gudanar da shirye-shiryen kur’ani a lokacin Arba’in Hosseini na kasar Iraki, a wannan shekara kuma sun gudanar da ayyukan wa’azi a cikin nau’ikan ayarin kur’ani na Arbaeen Darul Na’im.
Daga cikin shirye-shiryen da ya zuwa yanzu ‘yan kungiyar suka gabatar akwai karatun kur’akokin yabo ga manzon Allah da ahlul bait.
A ciki za a ga hotuna da bidiyo na yadda ‘ya’yan kungiyar mawaka da yabon Muhammad Rasoolullah (SAW) suka yi tatatkin Arbaeen.