Munanan Hare-Haren Isra’ila Sun Haifar Da Wata Sabuwar Gudun Hijira A Khan Yunus

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare masu muni  a yankunan tsakiyar Gaza da Khan Yunus, wanda hakan ya yi sanadiyyar kara samun hasarar rayuka

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai hare-hare masu muni  a yankunan tsakiyar Gaza da Khan Yunus, wanda hakan ya yi sanadiyyar kara samun hasarar rayuka tsakanin Falastinawa fararen hula masu yawa, da kuma haifar da wata sabuwar gudun hijira a yankin Khan Yunus.

Yakin kisan kare dangi na Isra’ila a kan al’ummar Gaza ya shiga rana ta 321, yayin da take ci gaba da kai wasu hare-haren a  dukkanin yankunan Zirin ta sama da kasa da ta ruwa.

Sakamakon hare-hare na baya-bayan nan da Haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan fararen hula da iyalan Falasdinawa a zirin Gaza, fararen hula hudu daga dangi daya sun yi shahada a arewacin sansanin Nuseirat da ke tsakiyar zirin Gaza, kuma wasu da dama da suka jikkata, an kuma kai wasu daga cikinsu asibitin Al Awda da ke arewacin sansanin.

A cikin birnin Gaza, unguwar Al-Zaytoun ta fuskanci hare-haren wuce gona da iri tare da ruwan bama-bamai da jiragen yaki, an kuma  kai wani harin da bindigogin atilari na sojojin Haramtacciyar kasar Isra’ila a kan gidajen mutane dake kan titin Kashko a unguwar Al-Zaytoun.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments