Sojojin HKI Sun Kai Manya-Manyan Hare-Hare A Kudancin Kasar Lebanon

Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa HKI ta kai hare hare a garin Bayut Al-Siyad da kuma Al-masuri ne saboda lalata rumbun ajiyar makamai

Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa HKI ta kai hare hare a garin Bayut Al-Siyad da kuma Al-masuri ne saboda lalata rumbun ajiyar makamai na kungiyar Hizbullah.

Jiragen yakin HKI sun kai hare hare kan wasu wurare a yankin Biqa na kudancin kasar Lebanon a jiya Litinin.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto wasu majiyoyin suna cewa mutum guda ya rasa ransa a harin a yayinda wasu 11 suka ji rauni. Amma gwamnatin kasar Lebanon ta ce mutane 8 ne suka ji rauni a hare haren na jiragen yakin HKI.

Amma a dayan bangaren kuma kungiyatr Hizbbullah tace ta kai hare hare kan sansanonin sojojin HKI da ke Beyaz Belida a arewacin kasar Falasdu da aka mamaye.

Kafafen yada labarai na HKI sun tabbatar da hare haren kungiyar Hizbulla, sun kuma kara da cewa jiragen ‘Drones’ masu kunan bakin wake ne guda 5 suka shiga yankin Galilee na sojojin kasar, inda suka sami nasarar kakkabo 3 daga cikinsu, amma biyu sun fada a kan wani sansanin sojoji ya kuma halaka bayahude guda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments