Hizbullah, Ta Yi Fatali Da Rahoton Jaridar WSJ, Kan Kisan Kwamandanta Fuad Shukr

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi watsi da wani labari da jaridar Wall Street Journal ta yi, wanda ya ambato yadda aka kashe babban

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta yi watsi da wani labari da jaridar Wall Street Journal ta yi, wanda ya ambato yadda aka kashe babban kwamandan kungiyar Fuad Shukr a ranar 30 ga watan Yuli, wanda a cewar jaridar an samu nakaso a fannin tsaro a cibiyar sadarwa ta Hizbullah.

An kashe kwamandan ne a wani hari da aka kai kan wani gini a wata unguwa mai cunkoso a kudancin birnin Beirut babban birnin kasar Lebanon wanda Isra’ila ta dauki alhakin kai harin.

Ita dai, jaridar ta Wall Street Journal ta yi ikirarin cewa an kashe kwamandan kungiyar ta Hizbullah ne bayan wani kira da aka yi masa aka  janyo shi daga ofishinsa zuwa gidansa mai hawa na bakwai, lamarin da ya sa aka kai masa hari cikin sauki.

Jaridar ta yi ikirarin cewa ta yi magana da wani jami’in Hizbullah, wanda ya ce kungiyar na gudanar da bincike kan na nakason da aka samu ta tsaro.”

A cikin wata sanarwa da ta fitar ta kafar sadarwa ta Telegram, Hezbollah ta ce labarin da jaridar ta buga ya kasance mai “cike da karya.”

Labarin, a cewar Hezbollah, wata manufa ce ta Isra’ila ta yada farfagandarta.”

Shugaban kungiyar Hizbullah Hassan Nasrallah, ya bayyana shahadar Shukr a matsayin “babbar hasara” amma ya tabbatar da cewa rashin nasa ba zai raunana kungiyar Hizbullah ba, kuma Kungiyar ta sha alwashin mayar da martani ga Isra’ila kan kisan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments