Iran Ta Shirya Tsab Don Zama Hanyar Wucewar Gas Na Kasar Rasha Zuwa Wasu Kasashe

Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta zama kasar da za’a wuce da gas na kasar Rasha zuwa sauran

Jakadan kasar Iran a Mosco ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta zama kasar da za’a wuce da gas na kasar Rasha zuwa sauran kasashe.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Kazem Jalali yana fadar haka a Mosco ya kuma kara da cewa, kasar Rasha a matsayin babbar kasa wacce Iran take huldar kasuwanci da ita, musamman a shekaru baya  bayan nan, tana da damar aiko da iskar gas dinta ya ratsa ta JMI zuwa wasu kasancen da ta sayarwa gas din a yankin Asia.

Jalali ya kara da cewa kasar Iran ta fara zama kasa wacce kayakin kasuwanci daga turai zuwa kasashen Asiya ta kudu zusu wuce ta cikinta, sannan da akasin haka, wato kayaki daga kasashen Asiya ma suna iya wucewa ta kasar zuwa kasashen turai ko kuma kasashen yamma a cikin yan watannin da suka gabata.

Shirin maida Iran a matsayin kasa, ko kuma  hanya ga kayakin kasuwanci na wasu kasashen yankin zuwa Turai, dai ya dade, amma gwamnatin marigayi shugaba Ra’isi ce ta karfafa shirin wanda kuma ya fara kankama a halin yanzu.

A cikin yan kwanakin da suka gabata ne jirgin kasa na farko dauke da kaya daga kasashen yankin zuwa kasar China ya fara wucewa ta kasar Iran.

Wannan shirin dai zai karya takunkuman tattalin arzikin da kasashen yamma musamman Amurka suka dorawa JMI don gurgunta kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments