Amurka Bata Bukatar Tsagaita Wuta A Gaza A Dai Dai Lokacinda Take Aikawa HKI Makamai Na Dalar Amurka Biliyon $20

Wani masanin harkokin siyasar gabas ta tsakiya, Abdul Bari Atwan ya zargi kasashen Larabawa musamman kasashen Masar da Katar da ha’inci, a lokacinda suka zama

Wani masanin harkokin siyasar gabas ta tsakiya, Abdul Bari Atwan ya zargi kasashen Larabawa musamman kasashen Masar da Katar da ha’inci, a lokacinda suka zama masu shiga tsakani don samar da yarjeniyar tsagaita wuta a Gaza, a dai dai lokacinda sojojin HKI suka aikata kissan kiyashi na Al-Dajar a Gaza.

Kamfanin dillancin labarai na Parstoday ya nakalto Abdul Bari yana fadar haka a jaridar Ra’ayul- Yau, inda ya yaba da shawarar da shugaban kungiyar Hamas Yayah  Sinwar ya dauka na rashin halattar taron tsagaita wuta na Doha, saboda ci gaba da kissan kiyashin da HKI take aikatawa a Gaza.

Abdul Bari ya kara da cewa manufar taron Doha na tsagaita wuta a Gaza, wanda William Burns shugaban hukumar CIA na kasar Amurka yake jagoranta, yaudara ce kawai, saboda kara jinkirta maida maratanin kasashen Iran da Hizbullah kan HKI sanadiyyar laifukan da ta aikata, wadanda suka hada da kashe marigayi shugaba kungiyar Hamas Isma’ila Haniyya a Tehran, da kuma Sayyid Fu’ad Shukur a birnin Beirut na kasar Lebanon.

Abdul Bari ya kara da cewa, shugabann kasar Amurka Joe Biden ba ya nufin samar da zaman lafiya a Gaza, kuma babban hujja iat ce aike da makamai wadanda yawanus ya kai dalar Amurka Billiyon 20 zuwa HKI.

Daga cikin makaman har da jiragen yaki samfuriun F-35 da wasu makamai masu kissan kiyashi, don HKI ta yi amfani da su a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments