Chaina Ta Ce Amurka Ce Babbar Barazana Ga Duniya Saboda Yawan makaman Nukliya Da Ta Mallak.

 Gwamnatin kasar Chaina ta bayyanan cewa Amurka ce babar barazana ga zaman lafiya a duniya musamman kan abinda ya shafi makaman Nukliya. Kamfanin dillancin labaran

 Gwamnatin kasar Chaina ta bayyanan cewa Amurka ce babar barazana ga zaman lafiya a duniya musamman kan abinda ya shafi makaman Nukliya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Zhang Xiaogang kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar China yana fadar haka, ya kuma kara da cewa Amurka ce kasa a duniya wacce ta mallaki makaman nukliya kuma take kokarin  tafiyar da duniyar ita kadai, don haka ita ce barazan babban idan an yi maganar makaman nukliya a duniya.

 Xiaogang yana maida martani ne ga shirin gwamnatin Amurka na kara kyautata sansanin sojojinta a kasar Japan zawa sansanin sojoji mai matsayin babban a yankin Asiya, wanda kuma jami’an sojoji masu tauraro 3 ne kawai zasu iya rike shi.

Karfafa sojojin Amurka a Japan wani al-amari ne na tunzurawa ga kasashen yankin musamman kasar China, saboda wannan shirin barazana ce ga tsaronta .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments