MDD Ta Yi Allawadai Da Yahudawan Sahyoniyya Da Suka Kaiwa Falasdinawa Hare Hare A Yankin Yamma Da Kogin Jordan

Kakakin hukumar kare hakkin bil’adana na MDD ta yi allawadai da yahudawan sahyoniya wadanda suka kai hare hare kan falasdinawa a kauyen Kalkeliya. Kamfanin dillancin

Kakakin hukumar kare hakkin bil’adana na MDD ta yi allawadai da yahudawan sahyoniya wadanda suka kai hare hare kan falasdinawa a kauyen Kalkeliya.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a ranar Alhamis ta da gabata ce yahudawan sahyoniyya kimani 100 suka farwa falasdinawa a kauyen Jis da ke kusa da garin Kalkeliy a yankin yamma da kogin Jordan inda suka kuna hemominsu da kuma motoci.

Labarin ya kara da cewa bafalasdine guda ya rasa ransa bayan da wani bayahude ya bude masa wutar bindiga a hare garen da suka kai masu a kauyen. Sannan wani guda ya ji rauni.

Labarin ya makalto Ravina Shamdasani mai Magana da yauwan hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD ta na fadar haka, ta kuma kara da cewa da alamun yahudawan basu yi haka ba, sai don isar da sako ga falasdinawan da kuma duniya kan cewa za su kwace karin yankunan Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan don ginawa yahudawa yan share wuri zauna gidaje.

A makon da ya gabata ma, yahudawan sun yiwa wasu Falasdinawa guda 4 dukan kawo wuka a yankin yamma da kogin jordan sannan sun jikata daya daga cikinsu har sai da aka kwanta asbiti.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments