Masana Sun Bayyana Dalilan Rashin Nasarar Amurka Kan JMI Don Tilasta Mata Mika Kai Ga Bukatunta

Wani mai bincike sannan marubuci mai suna Farid Zakariya ba’amerike kuma marubuci a jaridar Washington Post ya yi rubutu wanda jaridar ta buga, inda a

Wani mai bincike sannan marubuci mai suna Farid Zakariya ba’amerike kuma marubuci a jaridar Washington Post ya yi rubutu wanda jaridar ta buga, inda a ciki ya bayyana dalilan da suka sa gwamnatin Amurka ta kasa cimma manufofinta kan JMI duk tare da takunkuman tattalin arziki mafi muni da ta dorawa kasar a cikin tarihinta.

Zakariyya ya bayyana cewa a lokacin shugaba Barak Obama takunkuman tattalin arzikin da suka rage a kan Iran basu fi 370, amma bayan da shugaba  Donal Trump ya fice daga yarjiniyar JCPOA ya karasu zuwa 1,500, wanda ya maida Iran kasa wacce aka fi dorawa takunkuman tattalin arziki a duniya.

Zakariya ya ce kuskure na farko da Amurka ta yi shi ne kasashen Turai da dama basu amince da wasu takunkuman da Amurka ta dorawa Iran ba, sannan banda haka Iran ta yi amfani da damar da ta samu,  ta kara daga aikinta na makamashin nukliya zuwa kusa da samarda makamin Nukliya. Wasu jami’an gwamnatin Amurka sunce saura mata mataki guda ko matakai biyu kacal ta kera makaman nukliya.

Banda haka Iran ta kara karfafa dangantakarta da kasashe da kuma kungiyoyi masu gwagwarmaya a yankin, wadanda suka hada da Lebanon, Yemen, Iraki, Siriya da kuma Hamas, wadanda a halin yanzu sun zama hatsari babban ga samuwar HKI a yankin.  

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments