Hamas Tace Tsagaita Wuta Da HKI Dole Ne Ya Hada Da Janyewar Sojojin HKI Daga Gaza

Kungiyar Hamas wacce take gwagwarmaya da HKI tun ranar 7 ga watan Octoban da ya gabata a Gaza, ta kara jaddada cewa duk wata yarjeniyar

Kungiyar Hamas wacce take gwagwarmaya da HKI tun ranar 7 ga watan Octoban da ya gabata a Gaza, ta kara jaddada cewa duk wata yarjeniyar tsagaita wutan da za’a cimma da HKI a Gaza dole ne ya kai ga janyewar dukkan sojojin HKI daga zirin Gaza, da kuma dakatar da bude wuta gaba daya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar na bada wannan sanarwan a jiya Alhamis ta kuma kara da cewa musayar fursinoni kuma dole ne ya kasance gaba daya da gaba daya. Har’ila yau tace dole ne ya hada da sake gina zirin Gaza.

Hossam Badran wani jami’in kungiyar ya bayyana cewa tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Doha na kasar Qatar dole ne ya tashi daga inda aka tsaya a baya, inda aka yi maganar tsagaita wuta na din din din da kuma musayar fursinoni.

Yace duk wata yarjeniya da za’a cimma dole ne ta hada da tsagaita wuta, musayar fursinoni gaba daya, komawar mutane zuwa gidajensu a gaza da kuma sake gina Gaza.

Daga karshe ya ce kungiyarsa tana kan yarjeniyar watan Yulin da ya gabata, wanda ya sami amincewar kwamitin tsaro na MDD.

Kungiyar dai ta kauracewa taron tattaunawar tsagaita wuta na Doha ne saboda babutar hakan a lokacinda HKI take kissan kiyashi mafi muni a Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments