‘Yan Sahayoniyya Suna Gudanar Da Matsin Lamba Kan Kada A Fitar Da Sammacin Kama Netanyahu

Yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da daukan matakin matsin lamba a bayan fage don ganin an jinkirta sammacin kama Netanyahu da Gallant Hukumomin gwamnatin haramtacciyar

Yahudawan sahayoniyya suna ci gaba da daukan matakin matsin lamba a bayan fage don ganin an jinkirta sammacin kama Netanyahu da Gallant

Hukumomin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suna daukan matakan matsin lamba kan kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ke birnin Hague don hana fitar da sammacin neman kame fira ministan gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaronsa Yoav Galant bisa zargin aikata laifukan yaki a Zirin Gaza.

Jaridar Haaretz ta nakalto daga jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila da masu rajin kare hakkin bil’Adama suna tabbatar da cewa: Ana fuskantar matsin lamba ta diflomasiyya a bayan fage ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da nufin hana fitar da sammacin neman kama Netanyahu da Yoav.

Jaridar ta Haaretz ta yi nuni da cewa: Yana da wuya a iya hasashen irin tasirin da matsin lamban zai yi a kan kudurori da rukunin alkalan da suke bincikar shari’ar ta yahudawan sahayoniyya zai yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments