Duniya Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Kutsen Yahudawan Sahayoniyya Cikin Masallacin Al-Aqsa

Rashin amincewar kasashen Musulmi da tofin Allah tsine daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma sukar Amurka kan kutse yahudawan sahayoniyya cikin Masallacin Aqsa Amurka ta

Rashin amincewar kasashen Musulmi da tofin Allah tsine daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma sukar Amurka kan kutse yahudawan sahayoniyya cikin Masallacin Aqsa

Amurka ta soki kutsen da yahudawan sahayoniyya karkashin jagorancin ministan tsaron cikin gidan haramtacciyar kasar Isra’ila Itmar Ben Gvir suka yi cikin  harabar masallacin Al-Aqsa a jiya Talata, wanda Majalisar Dinkin Duniya, Tarayyar Turai da kasar Faransa suka yi Allah wadai da shi, yayin da kasashen musulmi suka yi Allah wadai da matakin yin kutsen, suna neman shiga tsakani na kasa da kasa.

Sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya ce, “Amurka na matukar adawa da ziyarar da ministan tsaron cikin gidan Isra’ila Itamar Ben Gvir ya kai masallacin Al-Aqsa da ke birnin Qudus.

Kakakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Farhan Haq ya bayyana cewa: Majalisar Dinkin Duniya tana adawa da duk wani yunƙuri na canza matsayi wurare masu tsarki, saboda nau’in dabi’a ne da ba zai zame mai amfani ba kuma lamari ne na tsokana.

Kungiyar Tarayyar Turai a ta bakin babban jami’I mai kulada harkokin wajen Tarayyar Turai Josep Borrell ta yi Allah wadai da tsokanar da ministan Isra’ila Ben Gvir ya yi, wanda a lokacin ziyararsa a wurare masu tsarki na musulmi ya yi kira da a keta haddin halin da ake ciki.

Ma’aikatar harkokin wajen Faransa ta ce, a cikin wata sanarwa da ta fitar, “Wannan sabon tsokana ba abu ne da za a amince da shi ba.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya yi kakkausar suka kan harin wuce gona da iri da wasu ministocin gwamnatin yahudawan sahayoniyya da wasu gungun tsagerun suka kai wa masallacin Al-Aqsa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments