An Samu Karuwar Shaye-Shaye A Tsakanin Sojojin Isra’ila – Bincike

Wani bincike da kwararru kan harkokin kiwon lafiya na yahudawan Isra’ila suka gudanar ya nuna cewa an samu karuwar shan miyagun ƙwayoyi da barasa da

Wani bincike da kwararru kan harkokin kiwon lafiya na yahudawan Isra’ila suka gudanar ya nuna cewa an samu karuwar shan miyagun ƙwayoyi da barasa da kuma wasu dabi’u na daban a tsakanin sojojin Isra’ila, suna masu alaƙanta ƙaruwar hakan da yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza na Falasdinu.

Isra’ilawan da kamfanin dillancin labarai na AFP ya zanta da su, sun ce suna amfani da ƙwayoyin ne a matsayin wani yunƙuri na guje wa gaskiyar abin da ke faruwa da mantawa da yaƙi da kuma kawar da fargabar da suke ciki.

Masanin ilimin lafiyar ƙwaƙwlwa Shaul Lev-Ran, wanda ya kafa Cibiyar Magance Jarabar Shan Ƙwaya ta Isra’ila (ICA), ya ce “a matsayin martani na dabi’a kan damuwa da kuma neman taimako, mun ga wani gagarumin tashin hankali a cikin amfani da wasu abubuwan kwantar da hankali da ke zama jaraba. ”

Wani bincike da tawagarsa ta gudanar ya gano “dangantaka tsakanin fallasa kai tsaye ga abubuwan da suka faru a ranar 7 ga Oktoba da kuma karuwar amfani da abubuwan maye” kusan kashi 25 cikin 100.

Lev-Ran ya ce ICA ta gano hauhawar amfani da “magani ba bisa ƙai’da ba da mugayen ƙwayoyi d, barasa, ko halayen jaraba kamar caca.”

A cikin 2022, ɗaya cikin bakwai na Isra’ilawa suna fama da jarabar shaye-shayen ƙwayoyi. Duk da haka, daya daga cikin Isra’ilawa hudu, tun daga lokacin, sun kara yawan amfani da kayan maye, bisa ga binciken, wanda aka gudanar a watan Nuwamba da Disamba na bara a kan samfurin wakilcin mutum 1,000 na Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments