Yahudawa Sun Afka A Cikin Masallacin Kudus Mai Alfarma

Isra’ilawa ‘yan kama-wuri-zauna ciki har da ministoci biyu sun kutsa cikin harbar Masallacin Birnin Kudus da ke Gabashin Kudus, tare da rakiyar dakarun Isra’ilam domin

Isra’ilawa ‘yan kama-wuri-zauna ciki har da ministoci biyu sun kutsa cikin harbar Masallacin Birnin Kudus da ke Gabashin Kudus, tare da rakiyar dakarun Isra’ilam domin gudanar da ibada. Lamarin ya harzuƙa Falasɗinawa Musulmai da ke harabar Masallacin.

Kamar yadda jaridar Ynet ta bayar da rahoto a shafin intanet , tace Ministan Tsaron Isra’ila mai ra’ayin rikau Itamar Ben-Gvir, da Ministan jam’iyyar Otzma Yehudit Yitzhak Wasserlauf da kuma mamba a majalisar dokokin Knesset a jam’iyyar Likud Amit Halevi sun bi sahun ‘yan kama-wuri-zauna kimanin 800 wajen shiga harabar masallacin inda suka yi addu’o’i na ibadar Talmud.

‘Yan kama-wuri-zauna sun shiga Masallacin Ƙudus ne domin yin biyayya ga kiraye-kirayen da Yahudawa masu tsattsauran ra’ayi suka a gare su don su gudanar da addu’o’i na bikin Tisha B’Av, wanda Yahudawa suke yi duk shekara don tunawa da bala’o’i daban-daban da suka faru a tarihin Yahudawa, in ji Wafa.

Sun shiga masallacin ne ta ƙofar yamma da ake kira Ƙofar Al-Mugharbah, wadda yawancin lokuta ake amfani da ita wurin shiga harabar masallacin, a cewar Wafa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments