Jagora Ya Jinjinawa Tawagar Iran Data Halarci Wasannin Olympics Na 2024

A daidai lokacin da ake kammala gasar wasannin Olympics a birnin Paris na na faransa, Jagoran Juyin Juya Halin Musulinci Na Iran, Ayatullah Sayyid Ali

A daidai lokacin da ake kammala gasar wasannin Olympics a birnin Paris na na faransa, Jagoran Juyin Juya Halin Musulinci Na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya mika godiyarsa ga ‘yan wasa da shugabannin kungiyoyi da masu horar da ‘yan wasa na kasar da suka halarci gasar.

Sakon na Jagoran juyin juya halin Musuluncin shi ne kamar haka;

“Da sunan Allah Madaukakin Sarki

Ina godiya kwarai da gaske ga ’yan wasa masu kima, masu kishi da kwarin gwiwa, shugabannin kungiyoyi da masu horarwa, da kuma kwamitin Olympics na kasa, wadanda suka kawo wa kasar farin ciki da daukaka a fagen wasanni a wannan gasa ta baya-bayan nan.

Tawagogin na Iran a gasar wasannin Olympics na bana sun samu lambobin yabo 12 (zinari 3 da azurfa 6 da tagulla 3) a wasan kokawa ta Greco-Roman da taekwondo da kuma matsayi na 21 a cikin kasashe sama da 200 da suka shiga gasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments