Aljeriya Ta Bukaci Zaman Gaggawa A Kwamitin Sulhu Na MDD Kan Harin Isra’ila A Gaza

Aljeriya ta yi kira da a gudanar da zaman gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata mai zuwa dangane da kisan

Aljeriya ta yi kira da a gudanar da zaman gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata mai zuwa dangane da kisan kiyashin da Isra’ila ta yi wa Falasdinawa a makarantar Al-Tabaeen da ke unguwar Al-Daraj a zirin Gaza.

Wata majiyar diflomasiyya ta Aljeriya daga kwamitin sulhu ta shaidawa kamfanin dillancin tass da hakan.

Majiyar ta nuna cewa har yanzu ba a amince da ranar da za a gudanar da zaman taron ba.

Harin bam din da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a makarantar “Al-Tabaeen” da ke  a unguwar Al-Daraj da ke gabashin birnin Gaza da safiyar ranar Asabar, ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan Palasdinawa 125 tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun ce an ruwaito cewa an kai harin ne a makarantar da ke unguwar Al-Daraj a tsakiyar Gaza a lokacin sallar Asuba.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi tsokaci kan harin bam da sojojin Isra’ila suka kai kan wata makaranta da ‘yan gudun hijirar ke fakewa a cikinta, lamarin da ya yi ajalin mutane fiye da 120 daga cikinsu tare da jikkata wasu da dama.

Farhan Haq, Mataimakin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar: “Bai kamata wuraren da ake amfani da su wajen tsugunar da ‘yan gudun hijirar su zama wurin kai hari ba.”

Ya jaddada cewa “dole ne a kiyaye dukkanin wuraren da ‘yan gudun hijirar suke kamar yadda dokar jin kai ta kasa da kasa ta tanada.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments