Shugaban Mauritaniya zai fuskanci manyan kalubale a wa’adin mulkinsa na biyu
Bayan shekaru 5 da Mauritaniya ta fuskanci mawuyacin halin tattalin arziki wanda ya haifar da hijirar matasa kusan 100,000, a halin yanzu wa’adin shugaban kasar Mohamed Wuld Ghazouani na biyu ya zo, wanda ya ce zai zama manufa mai cike da buri na yin gyare-gyare da gine-gine.
Duk da dimbin albarkatun da kasar take da shi, Mauritaniya mai yawan al’umma da ba su kai miliyan 5 ba, an kebe ta a matsayin daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya, yayin da mutane miliyan 2.3 (56.9% na al’ummar kasar) ke rayuwa cikin kangin mai tsanani, a cewar bayanai na Asusun Tallafawa kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF).
A shekara ta 2019, Ould Ghazouani ya gabatar da wani babban shiri da ya kira shi da “Alkawurana,” wanda a cikinsa ya himmatu wajen kawar batun fatara da talauci a kasar, amma karshen wa’adinsa na farko a watan Yulin da ya gabata, ya yi magana game da hadarin cin hanci da rashawa da kuma muhimmancin farfado da albarkatun kasa.
Baya ga matsalolin talauci, da rashin ci gaba a kasar, da matsalolin cin hanci da rashawa da gwamnati ta tabbatar da wanzuwarsu a kasar, Mauritaniya na fama da kalubalen siyasa na kasa da ke buƙatar yin aiki ta hanyoyi daban-daban kuma cikin sauri domin shawo kansu.