Kasar Burtaniya tana fuskantan rikici mafi muni tun kimani shekaru 13 da suka gabata.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto labaran da suke cewa wasu wandanda suke adawa da baaki yan kasashen waje wadanda suka zama yan kasa da kuma kin musulmi suna fara kai hare hare a kan wasu gine gina da kuma mutane baaki a kasar.
Labarin ya kara da cewa masu ra’ayin yan kasancin sun kai hare hare kan hotel hotel inda baki yan gudun hijira suke zama, da kuma wasu masallatai na musulmi, inda suke yin kira garesu na su fice daga kasar.
Sai dai Firai ministan kasar Burtania ta bada sanarwan cewa duk wanda aka kama zai hadu da fushin doka.
Ya zuwa yanzu dai an kama mutane kimani 400 wadanda ake zaton suna da hannu a cikin rikicin, kuma tuni an yakewa 3 daga cikinsu hukunci a kotu saboda sun bayyana kansa a kafafe yada labarai.
Wasu wadanda suka ganewa idansu sun bayyana cewa an fara rigimar ne bayan an dabawa yara 3 wuka a wata unguwa a kasar.
Wasu kuma suna danganta rigimar da ayyukan gwamnatocin kasar Burtaniya na fiye da shekaru 30 da suka gabata, na kaiwa wasu kasashen duniya hare hare kan karya. Da kuma dokokin da majalisar dokokin kasar suka kafa na yaki da ta’addanci da kuma sauransu.