Janar Musawi: Ba da jimawa ba Isra’ila za ta fuskanci babban martani kan kisan Haniya

Babban kwamandan rundunar sojin kasar Iran ya yi gargadin cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin Isra’ila za ta fuskanci martani mai karfi kan kisan

Babban kwamandan rundunar sojin kasar Iran ya yi gargadin cewa nan ba da jimawa ba gwamnatin Isra’ila za ta fuskanci martani mai karfi kan kisan gillar da ta yi wa shugaban kungiyar gwagwarmayar Falasdinu Ismail Haniyeh.

Manjo Janar Abdolrahim Mousawi ya bayyana hakan ne a yau  Laraba, kwana guda bayan da kungiyar Hamas ta zabi Sinwar mai shekaru 61 a matsayin shugaban kungiyar gwagwarmayar ta Hamas da ke da mazauni a Gaza, bayan kisan gillar da aka yi wa Haniyeh a babban birnin Tehran na Iran a makon jiya.

Mousawi ya bayyana Sinwar a matsayin “babban dan gwagwarmaya a wannan zamani “Wannan nadin na nuna hanyar da mayakan Palastinawa da Hamas suke da niyyar ci gaba da tafiya a kai, ta yadda gwamnatin sahyoniyawan ba ta da wani fata ga makomarta.”

Ya jaddada cewa ba za a iya samun nasara ba sai da gwagwarmaya da sadaukarwa.

Mousavi ya yi ishara da kisan gillar da Isra’ila ta yi wa Haniyeh inda ya ce, “Duk wannan yana nuna cewa a lokacin da gungun masu aikata laifuka da barna da yin watsi da dukaknin dokoki na duniya, suke samun goyon baya daga ido rufe daga manyan kasashe masu girman kai , da kuma shiru da gwamnatocin musulmi suke yi kan irin wanann barna da zubar da jinin yara da mata da fararen hula da yahudawan Isra’ila ‘yan ina da kisa suke yi, hakan babau abin da zai kara ma Haramtacciyar Kasar Isra’ila illa kwarin gwiwa wajen ci gaba da aikata irin wannan ta’asa.

Amma kuma a cewarsa, tabbas babu makawa harin ramuwar gayya na Iran a kan Isara’ila zai zamanto mai girgiza shika-shikan gwamnatin yahudawan ne.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments