Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah a kasar Labanon ta taya kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas da kuma sabon jagoranta Yahya Sinwar murnar zabensa da aka yi a matsayin shugaban ofishin siyasa na kungiyar, wanda ya maye gurbin Ismail Haniyeh, wanda “Isra’ila” ta kashe a makon da ya gabata a lokacin da yake ziyarar aiki a Iran.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, Hezbollah ta ce zaben Sinwar, wanda a halin yanzu yake tare da mayakan gwagwarmaya a Gaza a sahun gaba wajen yaki da mamayar Isra’ila a zirin Gaza, hakan ya tabbatar da cewa da yardarm za a cimma manufofin da aka sanya a gaba.
Bayanin ya ce wannan yana isar da sako mai karfi ga makiya, da kuma masu mara musu baya wato Amurka da kawayenta, cewa kungiyar Hamas kanta a hade yake dangane da wannan kuduri , tare da ci gaba da yin tsayin daka kan ka’idojinta, da zabinta, da kuma kudurin ci gaba da fafukar neman ‘yanci da fita daga kangi na mamayar haramtacciyar Kasar Isra’ila, wadda tare da taimakon turawa aka kirkiro ta kuma aaka kafa a ta a cikin kasar falastinu, kuma wannan sako na nasara ne wadda za ta tabbata ta hanyar juriya da sadaukarwa ta al’ummar falastinu da sauran musulmi da ‘yantattu masu mara baya ga gaskiya da neman tabbatar adalci a duniya.