MDD ta yi kira da a dauki matakin gaggawa domin shawo kan lamurra a yankin gabas ta tsakiya

Kwamishinan Kare Hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen tashe tashen hankula

Kwamishinan Kare Hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya yi kira da a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen tashe tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya, a daidai lokacin da ake fargabar yaduwar yakin Gaza a yankin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ya bayyana cewa, “Na damu matuka game da yadda ake fargabar kara samun barkewar rikici a Gabas ta Tsakiya, inda ya yi kira ga dukkan bangarorin, tare da kasashe masu tasiri, da su dauki matakin gaggawa don kwantar da hankula.”

Ya tunatar da bangarorin cewa hakkin dan Adam da kare fararen hula dole ne su kasance a gaba, yana mai jaddada cewa fararen hula, wadanda akasarinsu mata ne da kananan yara, sun riga sun sha wahala da ba za su iya jurewa ba, sakamakon tashin bama-bamai da makamai a watannin da suka gabata.

“Dole ne a yi duk abin za a iya yi, don gujewa fadawa cikin wannan yanayi da zai haifar da mummunan sakamako ga fararen hula,” in ji kwamishinan kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya.

Arangama tsakanin kungiyar Hizbullah ta Labanon da Isra’ila ta kara ta’azzara tun bayan da Tel Aviv ta kashe wani babban kwamandan sojin kungiyar  Fouad Shukr a wani hari ta sama da aka kai a wata unguwa da ke birnin Beirut a ranar 30 ga watan Yuli.

Sannan kuma an kashe shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh a Tehran babban birnin kasar Iran washegari, a wani hari da aka dorawa Isra’ila alhakin kai wa, wanda kuma bat a kore hakan ba.

Yanzu dai ana cikin zaman dardadra  yankin gabas ta tsakiya, saboda rashin sanin irin martanin da Iran da Hizbullah da kawayensu za su mayar kan yahudawan Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments