Firai ministar Bangladesh Sheikh Hasina ta yi murabus tare da tserewa daga kasar a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da manufofin gwamnatinta da kuma salon mulkin da suka kira na kama karya.
Matar mai shekaru 76 ta bar Dhaka babban birnin kasar a cikin wani jirgin sama mai saukar ungulu na soja tare da ‘yar uwarta a wannan Litinin.
Kafofin yada labarai daban-daban sun ce ta gudu zuwa Indiya don neman mafaka a can.
An fara zanga-zangar ne a watan da ya gabata bayan da kasar ta sake bullo da wani shiri da ake kira rabon kaso wanda ya kebe fiye da rabin ayyukan gwamnati ga wasu kungiyoyi.
Zanga-zangar al’ummar kasar ta gudana ne domin neman kawo karshen mulkin Hasina na tsawon shekaru 15.
Akalla mutane 300 ne aka ce an kashe a zanga-zangar, wadda it ace mafi muni da kasar ta gani cikin shekaru sama da hamsin.
A ranar jiya Lahadi ne aka yi mummunar arangama tsakanin jami;an tsaro da kuma masu zanga-zangar, inda aka bayar da rahoton cewa kimanin mutane 94 ne suka rasa rayukansu a jiya.
Jami’an tsaro sun goyi bayan gwamnatin Hasina a lokacin zanga-zangar. Amma a yau Litinin babban hafsan sojin Bangladesh Waker-Uz-Zaman ya ce Hasina ta sauka kuma ta bar kasar, kuma zai kafa gwamnatin wucin gadi.