Kungiyar ta’addanci ta Al-Shabab mai tsaurin ra’ayi ta kai wani harin kunan bakin wake tare da bude wutar bindiga kan al’ummar Somaliya a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar a yammacin ranar Juma’a lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 32, tare da jikkatan wasu da dama a yankin gabar tekun da ‘yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati ke yawan zuwa a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar.
Kakakin ‘yan sandan kasar Abdel Fattah Aden Hassan ya shaida wa manema labarai cewa: Fiye da fararen hula 32 ne aka kashe a wannan harin, kuma wasu 63 ne suka jikkata, sannan wasu daga cikinsu sun samu munanan raunuka.”
‘Yan sanda da shaidun ganin ido sun bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a jiya Asabar cewa: Wani dan kunar bakin wake da ya yi jigida da bama-bamai ya tarwatsa kansa a yammacin ranar Juma’a a bakin tekun Liido, wanda ‘yan kasuwa da ma’aikatan gwamnati ke yawan zuwa a wata unguwa mai cike da manyan otal-otal da manyan gidajen cin abinci, wanda wannan wurin ya fuskanci hare-haren ta’addanci a baya.