Shugaban Ma’aikatar Shari’ar Iran Ya Jaddada Cewa: Kalmomi Ba Zasu Iya Kwatanta Laifuka ‘Yan Sahayoniyya Ba

Shugaban Ma’aikatar Shari’ar kasar Iran ya jaddada cewa: Kalmomi ba za su iya kwatanta laifukan da ‘yan sahayoniyya suka aikata ba Shugaban ma’aikatar shari’a ta

Shugaban Ma’aikatar Shari’ar kasar Iran ya jaddada cewa: Kalmomi ba za su iya kwatanta laifukan da ‘yan sahayoniyya suka aikata ba

Shugaban ma’aikatar shari’a ta kasar Iran Hujjatul -Islam Gholam Hossein Mohsini Ejei ya bayyana cewa: A yau kalmomi ba za su iya bayyana laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa ba, kuma ba za a iya bayyana irin wadannan muggan laifuka ba ta hanyar amfani da kalmomi irin na zalunci da kisan gilla kan bil’Adama musamman yara da mata ko kuma wata gwamnatin masu dabi’un dabbobi da suke aikata laifukan yaki ba.

Hujjatul -Islam Gholam Hossein Mohseni Ejei ya bayyana haka ne a wajen bikin tunawa da ranar kare hakkin bil’adama da martabar musulmi da kuma raba lambar yabo ta Musulunci karo ta takwas a birnin Tehran: Yana mai jaddada cewa: Yawancin al’ummar duniya a kasashe daban-daban, hatta a kasashen da ke goyon bayan ayyukan laifuka yahudawan sahayoniyya da suka hada da Amurka masu aikata laifuka, sun fahimci ayyukan wannan gwamnatin ‘yar mamaya ta karya, amma hakan bai wadatar ba, kuma dole ne masu kare hakkin bil’adama na Musulunci su dauki kwararan matakai na tona asirin laifukan ‘yan sahayoniyya.

A gefe guda kuma, wadanda suka samu nasarar lashe lambar yabo ta kare hakkin bil’Adama ta Musulunci sune: Shugaban ofishin siyasa na Hamas, Isma’il Haniyeh, babban sakataren kungiyar Jihadul-Islami ta Falastinu, Ziyad Nakhalah, tsohon shugaban kungiyar Jama’atul Islamiyyah ta Pakistan, Siraj al-Haq, da kuma lauyan Faransa kuma mai fafutukar kare hakkin bil’adama, Gilles Defer, mai fafutukar kare hakkin dan Adam kuma mai yaki da ‘yan sahayoniyya a Kanada, Charlotte Kates, da kuma jakada kuma wakili na dindindin na kasar Nicaragua a Majalisar Dinkin Duniya, Jaime Hermida Castillo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments