Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Bayyana Cewa Iran Zata Koya Wa Yahudawan Sahayoniyya Darasi

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Za su koya wa haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka darasi a rayuwa Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya bayyana cewa: Za su koya wa haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka darasi a rayuwa

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf, ya tabbatar da cewa: Amurka da yahudawan sahayoniyya za su yi nadamar matakin da suka dauka na kashe shahidi Isma’il Haniyyah.

Qalibaf ya ci gaba da cewa, a yayin taron majalisar shawarar Musulunci ta yau Lahadi, dadin bikin dimokaradiyya mai farin jini da aka yi a wajen bikin rantsar da shugaban kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya koma bakin ciki saboda shahadar shugabanni biyu na bangaren gwagwarmaya musamman a lokaci daya daga cikin wadannan shahidai guda biyu shi ne Isma’il Haniyeh wanda ya kasance bakon Iran kuma ya yi shahada ne a cikin gidan Iraniyawa.

Shugaban Majalisar Shawarar ta Musulunci ya kara da cewa: Ko shakka babu, bayan faruwar wannan lamari mai daci, al’ummomi da ‘yantattun kasashen duniya da dakarun gwagwarmaya sun shiga cikin bakin ciki mai tsanani amma lallai za su koma cikin farin ciki da annashuwa sakamakon martani mai gauni da Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata mayar kan haramtacciyar kasar Isra’ila tare da wurga ta cikin nadama da masu goya mata baya musaman Amurka.

Shugaban Majalisar Shawarar ta Musulunci ya ci gaba da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta taba mantawa da cewa, bayan gudanar da harin daukan fansa na Falasdinawa na Ambaliyar Al-Aqsa,                                   muhimman ayyuka da shirye-shiryen yahudawan sahayoniyya suka ruguje, kuma hasken farko na bayyana karshen wanzuwarta ya kunno kai, sannan saboda gazawar manufofin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanya a gaba tsarin tsaronta da manufofin siyasarta sun wargaje don haka ta shiga cikin kangin rikicewa da rashin nutsuwa da zasu hanzarta kai ta ga tarwatsewa cikin gaggawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments