Yahudawan Sahayoniyya Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Kin Jinin Fira Ministan Netanyahu  

Yahudawan Sahayoniyya sun gudanar da zanga-zanga a filin jirgin saman Ben Gurion kafin Netanyahu ya tashi zuwa kasar Amurka Rahotonni sun bayyana cewa: Daruruwan yahudawan

Yahudawan Sahayoniyya sun gudanar da zanga-zanga a filin jirgin saman Ben Gurion kafin Netanyahu ya tashi zuwa kasar Amurka

Rahotonni sun bayyana cewa: Daruruwan yahudawan sahayoniyya ne suka gudanar da zanga-zanga a filin jirgin saman Ben Gurion da ke Tel Aviv domin neman kulla yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila karkashin jagorancin fira minista Benjamin Netanyahu a yayin da fira ministan ke shirin tashi a yau Litinin zuwa birnin Washington na Amurka.

Rahotonni sun bayyana cewa: Mahalarta zanga-zangar sun yi kira ga Netanyahu da kada ya kai ziyara zuwa Amurka, har sai ya sanya hannu kan yarjejeniyar sakin fursunonin yahudawa 120 da suke hannun ‘yan gwagwarmaya a Gaza.

‘Yan sandan gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun kasance a wurin da aka gudanar da zanga-zangar domin tarwatsa masu zanga-zangar da suke neman kawo cikas ga tafiyar Netanyahu.

A cikin wannan yanayi, an yi taho-mu-gama tsakanin masu adawa da gwamnatin Netanyahu da masu goya mata baya a birnin Tel Aviv a lokacin zanga-zangar neman kammala yarjejeniyar musayar fursunonin tare da neman kawo karshen gwamnatin Benjamin Netanyahu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments