Kungiyar Gwagwarmayar Musulunci Ta Hizbullah Ta Kai Hare-Hare Kan Sojojin Isra’ila

A cikin kasa da sa’o’i 12 da suka gabata, mayakan kungiyar Hizbullah sun kai hare-hare sau 12 kan sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar

A cikin kasa da sa’o’i 12 da suka gabata, mayakan kungiyar Hizbullah sun kai hare-hare sau 12 kan sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da aiwatar da wasu jerin hare-hare kan haramtacciyar kasar Isra’ila tare da yin amfani da makamai nau’i daban-daban, gami da tabbatar da cewa hare-haren sun kai daidai yadda aka saita su.

Kungiyar Hizbullah ta jaddada cewa: Domin jaddada nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu da jajircewar ‘yan gwagwarmaya a Zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmaya kare kai da neman hakki, mayakanta sun yi ruwa makamai masu linzami kan muhimman wurare a haramtacciyar kasar Isra’ila musamman na sojojin yahudawan sahayoniyya.

Majiyar kungiyar ta bayyana cewa: ‘Yan gwagwarmayar kungiyar ta Hizbullahi sun kai hare-hare kan yankin Al-Sammaqa da ke tsaunin Kufur Shuba kan sansanin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila da makamai masu linzami, kuma hare-haren sun samu yadda aka saita su kai tsaye.

Kamar yadda mayakan kungiyar suka kai hare-hare kan sansanin sojin yahudawan sahayoniyya na Ruwaisat al-Qarn da ke gonakin Sheb’a na kasar Labanon da aka mamaye da makamai masu linzami.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments