Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Ce: Taron Juyayin Ashura Yana Firgita Azzalumai

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Taron juyayin Ashura Imam Hussaini lokaci ne na tona asirin ‘yan ta’addar sahayoniyya Kakakin ma’aikatar harkokin wajen

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Taron juyayin Ashura Imam Hussaini lokaci ne na tona asirin ‘yan ta’addar sahayoniyya

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana cewa: A ranar Ashura Imam Huseini {a.s}, an yi kirar da a tallafa wa kananan yara da matan Falastinawa da ake zalunta, tare da fallasa muggan laifukan ta’addancin gwamnatin yahudawan sahayoniyya da masu goya musu baya.

A rubutunsa a shafinsa na sada zumunta, Nasir Kan’ani ya mika sakon ta’aziyyar Ashurar Imam Hussaini {a.s} ga daukacin musulmi da ‘yan Shi’a da ‘yantattun al’ummar duniya, yana mai cewa: Imam Husaini (a.s) shi ne ma’auni na tsayuwa ga Allah kuma mafi daukakan kyawawan dabi’u da aiwatar da dabi’un dan Adamtaka, da tawaye ga azzalumai da rashin mika wuya ga ‘yan tawaye da shaidanun duniya.

Ya ci gaba da cewa: A ranar Ashurar Imam Husaini {a.s}, an bukace mu da mu daukaka al’adun Ashura, mu tallafa wa yara da mata na Falastinu da ake zalunta, da kuma fallasa sharri da ta’addanci na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da masu goyon bayan wannan haramtacciyar kasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments