Tsohon shugaban kwamitin tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila, Manjo Janar Giora Eiland, ya ce: Haramtacciyar kasar Isra’ila tana fuskantar wani yaki a yau fiye da wanda ta fuskanta a yakin shekara ta 2014, saboda matsayinta na dabarun yaki sun tabarbare bayan shekaru goma don yadda Iran da kawayenta suka karfafa matsayinsu.
A wani bangare na nazarinsa kan halin da ake ciki a yanzu, da kuma tsaka mai wuya da haramtacciyar kasar Isra’ila ta shiga sakamakon harin daukan fansa Ambaliyar Al-Aqsa, Janar Giora Eiland mai ritaya ya fadawa jaridar Yedioth Ahronoth ta haramtacciyar kasar cewa: Yakin da ake yi a Zirin Gaza a yau ya fi na yakin Gaza da aka yi a shekara ta 2014 tsanani da wahala.
Yana mai cewa: Har zuwa lokacin kai harin ranar 7 ga watan Oktoban bara, yakin shekara ta 2014 shi ne yaki mafi tsayi tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da sojojin mamayar haramtaccoyar kasar Isra’ila, yayin da a lokacin yakin aka shafe tsawon kwanaki 51 ana gwabza fada, kuma yakin ya yi sanadin shahadar Falasdinawa sama da dubu biyu, kuma sama da dubu 8 suka jikkata. Sannan yakin ya lashe rayukan sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila 68.