Da yawa daga cikin iyalan Falasdinawa da suke birnin Qudus suna fuskantar barazanar tilasta musu yin hijira daga muhallinsu
Malamin addinin Kirista Al-Maqdisi Kayed Al-Rajabi ya yi magana kan rikicin shari’a da ya ƙare kan neman korarsu daga muhallinsu da ke unguwar Batn al-Hawa a cikin garin Silwan don goyon bayan tsagerun yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida da suka kawo takardun jaje da suke neman tilastawa Falasdinawa kimanin iyalai 75 barin muhallinsu a unguwar da suke rayuwa.
Bayan doguwar shari’a, iyalai gidan Al-Rajabi mazauna birnin Qudus, da suka kai mutane 27, suna jiran lokacin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila zata dauki matakin aiwatar da shawarar raba su da muhallinsu domin mallaka wa yahudawan sahayoniyya ‘yan kaka gida.
Kayed Al-Rajabi, mamba ne na kwamitin unguwar Batn al-Hawa da ke garin Silwan a birnin Qudus, kuma mai gidan da ke cikin hadarin kwacewa, ya ce danginsa na zaune a gidan tun shekara ta 1965, kuma shi tun a shekara ta 2009 ne ake gwabza rikicin neman raba shi da muhallansu, amma hukuncin da kotun haramtacciyar kasar Isra’ila ta yanke a wancan lokacin ya kasance mai ban sha’awa, idan ta tabbatar da cewa takardun da yahudawan sahayoniyya suka gabatar kan mallakar gidan na jabu ne wanda ke nuna gidan mallakinsa ne tun kafin shekara ta 1948. Ya kara da cewa: Yanzu haka Falasdinawa da suka kai iyalai 75 da suke zaune a yankin suna fuskantar kora daga unguwar ta Batn al-Hawa.