Shugaban Iran Ya Ce Ba Zasu Bar Al’ummar Falasdinu Ita Kadai Ba Cikin Mawuyacin Hali

Shugaban kasar Iran ya bayyanawa shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas cewa: Ba za su bar al’ummar Falasdinu su kadai ba a cikin wannan mawuyacin hali

Shugaban kasar Iran ya bayyanawa shugaban ofishin siyasar kungiyar Hamas cewa: Ba za su bar al’ummar Falasdinu su kadai ba a cikin wannan mawuyacin hali

Shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniyeh, ya zanta da zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ta hanyar wayar tarho, inda suka tattauna batutuwan siyasa da na yaki da suka shafi aniyar yahudawan sahayoniyya na neman rusa yankin Zirin Gaza kwata-kwata da kuma ci gaban da ake samu da suka shafi batun Falasdinu.

Isma’il Haniyeh ya kuma sake taya shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian murnar zaɓen da aka yi masa a matsayin shugaban ƙasar Iran a zaɓen da al’ummar Iran suka bayyana darajar demokradiyya da girmama ra’ayin al’umma ta hanya mafi kyau. Haka nan Haniyeh ya sanar da shugaban Iran yadda yahudawan sahayoniyya suke yunkurin aiwatar da kisan kiyashi kan al’ummar Falasdinu musamman ta hanyar kashe-kashe kan fararen hula misalin kashe-kashen kiyashi da suka yi kan al’ummar birnin Kham Yunus da na Al-Shati a shekaran jiya bisa zargin karya cewa, ana kai hare-haren ne kan jagororin ‘yan gwagwarmaya, yana mai jaddada cewa: Wannan kashe-kashen gillar ya zo ne bayan kyakkyawar niyyar da kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa suka nuna a zaman tattaunawan neman dakatar da bude wuta, inda fira ministan yahudawan sahayoniyya Benjamin Netanyahu ya gindaya wasu karin sabbin sharudda da ba su cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu musamman kan batun musayar fursunoni, lamarin da ke nuni da cewa: Netanyahu ya fi son cigaba da gudanar da yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments