Gungun ‘Yan Leken Asirin Amurka DaAka Kama A Yemen Sun Tona Asiri Masu Yawa

Sabbin ikirari da gungun ‘yan leken asirin Amurka suka yi sun fayyace mummunar makircin da makiya suke kitsawa kan kasar Yemen Furucin da gungun ‘yan

Sabbin ikirari da gungun ‘yan leken asirin Amurka suka yi sun fayyace mummunar makircin da makiya suke kitsawa kan kasar Yemen

Furucin da gungun ‘yan kungiyar leken asirin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila suka yi yana tabbatar da cewa Amurka ta tunkari yin kutse a tsakanin kabilun Yemen da nufin rusa muhimmiyar rawar da suke takawa a tsawon tarihinsu wajen dakile makirce-makircen mahara da suke son rusa mutuncin kasar Yemen da ‘yancin kanta.

Ikirarin ‘yan kungiyar leken asirin, wanda jami’an tsaron Yemen suka wallafa yana bayyana cewa: A baya an wasan kura da kabilun Yemen da cusa kwadayi a zukatan shehunnai da masu fada a ji a cikin al’umma, ta hanyar gwamnatin Saudiyya da kwamitinta na musamman da hakan ya zame amfanin Amurka da kare masalarta, sannan Amurka ta yunkuro kai tsaye don kalubalantar kabilun Yemen tare da kokarin kutsawa cikinsu da daukar wasu shehunnai da wasu mutane masu tasiri musamman a tsakanin kabilu da suke muhimman yankunan kasa da suke dauke da tarin arzikin mai.

Daga cikin ‘yan leken asirin Abdul Mo’ein Azzan ya bayyana cewa: Shirin magance rikice-rikice, ko kuma abin da ake kira shirin sulhunta kabilun a cikin gida, yana karkashin kulawar wani ma’aikaci dan kasar Yemen mai suna “Nada Al-Dosari,” kuma shirin an gina shi ne a kan rusa tasirin gwagwarmayar kabilu da shehunan kabilunsu da suke shiga tsakani don sasanta duk wani sabanin kabilun kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments