Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Yi Watsi Da Zargin Kungiyar Tsaro Ta NATO Kanta

Kasar Iran ta musanta zargin da kungiyar tsaro ta NATO ke yi kanta na taimakawa Rasha a yakin da take yi da kasar Ukraine Kakakin

Kasar Iran ta musanta zargin da kungiyar tsaro ta NATO ke yi kanta na taimakawa Rasha a yakin da take yi da kasar Ukraine

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasir Kan’ani ya bayyana a yau Alhamis cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da zargin da ke kunshe a cikin bayanin karshe na taron kungiyar tsaro ta NATO da aka gudanar a birnin Washington na kasar Amurka na cewa Iran tana aikewa da kayayyakin soji zuwa kasar Rasha a matsayin taimaka mata a yakar Ukraine da take yi, tare da daukar zargin a matsayin maras tushe mai dauke da manufar siyasa.

Dangane da wani bangare na bayanin taron kolin kungiyar tsaron ta NATO da aka gudanar a birnin Washington; Kan’ani ya bayyana takaicinsa da cewa abin da ake gani a kasar Ukraine ya samo asali ne sakamakon manufofi da matakan tsokana na kungiyar tsaro ta NATO, wadanda tushensu Amurka ce, kuma har yanzu suke ci gaba da gudana cikin sauri.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya ci gaba da cewa: Kamar yadda Iran ta sha bayyana cewa: Duk wani yunkuri na alakanta yakin kasar Ukraine da hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kasar Rasha, wani lamari ne na siyasa da neman tunzura al’umma, kuma manufarsa ita ce karfafa shisshigin da ake yi da ci gaba da gabatar da agajin soji na yammacin Turai ga kasar Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments