Ma’aikatar Lafiyar Gaza: Adadin Falastinawa da suka yi shahada a hare-haren Isra’ila ya kai 38,295

Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kaiwa yankin tun

Ma’aikatar lafiya a zirin Gaza ta sanar da cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kaiwa yankin tun ranar 7 ga watan Oktoba ya kai mutane 38,295.

Ma’aikatar ta ce a cikin rahotonta na kididdiga ta yau da kullun, “Mamayakan Isra’ila sun yi kisan kiyashi 4 kan iyalai a zirin Gaza, ciki har da shahidai 52 da jikkata 208 a cikin sa’o’i 24 da suka gabata.”

Ta kara da cewa, “Har yanzu akwai adadin wadanda abin ya rutsa da su a karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, kuma motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaron farar hula ba za su iya isa gare su ba.”

Ta yi nuni da cewa, “yawan yawan hare-haren wuce gona da irin na Isra’ila ya karu zuwa shahidai 38,295 da kuma jikkata 88,241 tun daga ranar bakwai ga watan Oktoban bara.”

Ma’aikatar ta yi kira ga iyalan shahidai da wadanda suka bata a yakin Gaza da su kammala bayanansu ta hanyar yin rijista ta hanyar da aka makala, domin cika dukkan bayanan ta bayanan ma’aikatar lafiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments