Isra’ila tana kara tsananta hare-harenta a wurare masu kariya bisa dokoki na kasa d akasa

Isra’ila tana kara tsanta hare-hare a wurare masu kariya bisa dokoki na kasa a cikin yankunan zirin gaza, kamar yadda bangarori na kasa da kasa

Isra’ila tana kara tsanta hare-hare a wurare masu kariya bisa dokoki na kasa a cikin yankunan zirin gaza, kamar yadda bangarori na kasa da kasa suka tabbatar da hakan.

Sojojin Isra’ila sun yi kisan kiyashi a makarantar Al-Awda da ke garin Abasan na gabashin Khan Younis, a cewar wata sanarwa da Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta fitar.

Galibin yankunan Birnin Gaza sun kasance tamkar kufayi sakamakon luguden wutar da dakarun Isra’ila suka kwashe watanni tara suna yi a yankin. Yawancin mutanen da ke birnin sun tsere tun da aka fara yaƙin, amma dubban mutane na ci gaba da zama a arewaci.

A watanni tara da Isra’ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, dakarunta sun mamaye asibitoci aƙalla takwas, inda suka kashe majinyata da ma’aikatan kiwon lafiya tare da lalata gine-gine da kayan aiki.

Isra’ila ta yi zargin cewa ƙungiyar Hamas tana mafani da asibitocin ne domin ajiye makamai, ko da yake ba ta bayar da cikakkun shaidu game da zargin nata ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments