Al’Sisi Ya Taya Pezeshkian, Murnar Lashe Zaben Iran

Kasar Masar ta bi sahun kasashen dake aikewa da sakon taya zababben shugaban kasar Masoud Pezeshkian murna a matsayin sabon shugaban ƙasar Iran. A cewar

Kasar Masar ta bi sahun kasashen dake aikewa da sakon taya zababben shugaban kasar Masoud Pezeshkian murna a matsayin sabon shugaban ƙasar Iran.

A cewar sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar Masar Ahmed Fahmy ya fitar, shugaba Abdel Fattah el-Sisi ya aike da sakon taya murna ga zababben shugaban kasar Iran Pezeshkian, yana mai cewa nasarar da ya samu na nuni da irin kwarin gwiwar da al’ummar Iran suke da shi na iya yin hidima ga kasarsa.

Sisi ya kuma yi wa sabon shugaban fatan samun nasara a ayyukansa tare da nuna jin dadinsa ga kyakkyawar alakar da ke tsakanin al’ummar Masar da Iran.

Kafin nan Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana son yin hadin gwiwa da zababben shugaban kasar ta Iran Pezeshkian.

Mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric, ya ce kungiyar na son yin hadin gwiwa da sabon shugaban kasar Iran.

“Muna fatan yin aiki tare da sabon shugaban Iran,” in ji shi a wani taron manema labarai.

Pezeshkian, mai shekaru 69 da haihuwa, ya lashe zaben shugaban kasar zagaye na biyu da kuri’u sama da miliyan 16.3.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments