Pezeshkian : Ba Za Mu Yi Kasa A Gwiwa Ba Wajen Goyon Bayan ‘Yan Gwagwarmaya

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce gwamnatinsa mai jiran gado ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da goyon baya

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce gwamnatinsa mai jiran gado ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bayar da goyon baya ga ga ‘yan gwagwarmaya ba a yammacin Asiya, yana mai jaddada cewa goyon bayan kungiyoyin ya samo asali ne daga muhimman manufofin Jamhuriyar Musulunci.

A cikin wani sako da ya aikewa babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Labanon Sayyed Hassan Nasrallah, Pezeshkian ya mika godiyarsa ga sakon da ya samu na taya shi murna nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar Iran da aka gudanar a ranar 5 ga watan Yuli.

Zababben shugaban na Iran ya ci gaba da cewa Tehran tana goyon bayan tsayin daka da al’ummomin yankin suke yi a kan ‘yan sahyoniya.

Pezeshkian ya kara da cewa kasarsa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga bangaren tsayin daka kamar yadda ya samo asali daga muhimman manufofin Iran, da manufofin marigayi Imam Khumaini da jagororin jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwar cewa kungiyoyin gwagwarmaya a yankin ba za su bari gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da aiwatar da manufofinta na yaki da ta’addanci kan Falasdinawa da ake zalunta da sauran kasashen yankin ba.

Shi ma shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu Ismail Haniyeh, ya taya Pezeshkian murnar lashe zaben shugaban kasar Iran da kuma yadda aka gudanar da zaben.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments