Al’ummar Iran, Na Kada Kuri’a A Zaben Shugaban Kasa Zagaye Na Biyu

Al’ummar Iran sun fara kada kuri’a a zaben shugaban kasar zagaye na biyu. An bude rumfunan zaben a karfe 8 na safiyar yau Juma’a agogon

Al’ummar Iran sun fara kada kuri’a a zaben shugaban kasar zagaye na biyu.

An bude rumfunan zaben a karfe 8 na safiyar yau Juma’a agogon kasar (04:30 GMT) kuma an shirya rufe rumfunan zaben a karfe 6:00 na yamma, (1430 GMT).

Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya kada kuri’arsa a wata rumfar zabe da ke birnin Tehran a daidai lokacin da aka fara kada kuri’a.

A ranar Lahadi ne aka fara yakin neman zaben zagaye na biyu, daidai bayan da ma’aikatar harkokin cikin gida ta sanar da sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 28 ga watan Yuni.

‘Yan takara Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili ne suka fi yawan kuri’u, amma duk da haka babu wanda ya yi nasarar samun gagarumin rinjaye, lamarin da ya sa ake je zaben a zagaye na biyu.

Sama da mutane miliyan 24 ne suka fita zaben zagaye na farko a ranar 28 ga watan Yuni.

Zaben dai na neman nada wanda zai gaji shugaba Raeisi wanda ya rasu a ranar 19 ga watan Mayu a wani mummunan hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu.

Cibiyar zaben kasar, Ta ce za a iya bayyana sakamakon farko na zaben zagaye na biyu da safiyar gobe Asabar.

Kimanin mutane miliyan 61 ne suka cancanci kada kuri’a, kamar yadda hedkwatar zaben ta tabbatar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments