Wasu Falastinawa 4 ‘Yan Gwagwarmaya Sun Yi Shahada A Wani Harin Isra’ila a Tulkaram

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kashe mayakan Falastinawa  ‘yan gwagwarmaya  4 ta hanyar jefa bama-bamai a sansanin Nour Shams da ke gabashin Tulkarm a

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kashe mayakan Falastinawa  ‘yan gwagwarmaya  4 ta hanyar jefa bama-bamai a sansanin Nour Shams da ke gabashin Tulkarm a gabar yammacin kogin Jordan, yayain da kuma sauran bangarorin ‘yan gwagwarmaya suka sha alwashin  mayar da martani mai zafi kanj Isra’ila.

Mayakan gwagwarmayar Falasdinawa hudu sun yi shahada ne  a daren ranar jiya, a wani harin da jiragen saman sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila suka kai sansanin Nour Shams, dake gabashin Tulkarm a gabar yammacin kogin Jordan.

Dakarun Al-Quds Brigades, da na Al-Qassam Brigades, da na Al-Aqsa Brigads na Tulkarm, sun jadda a cikin wani bayani na hadin gwiwa  ga al’ummar Palastinu cewa, wannan kisan gilla babu abin zai kara musu illa ci gaba kwarin kwarin gwiwa ga zabin da ke gabansu na gwagwarmaya da yahudawan sahyuniya ‘yan mamaya, kuma sun sha alwashin mayar da martani mai zafi kan kisan ;yan gwagwarmaya hudu da sojojin yahudawan suka yi.

Wadanda suka yi shahada su ne: Yazid Saed Adel Shafi’a (mai shekaru 22), Nimr Anwar Ahmed Hamarsheh (mai shekaru 25), Muhammad Yasser Raja Shehadeh (mai shekaru 20), da Muhammad Hassan Ghannam Kanouh (mai shekaru 22).

Dakarun Kudus Brigade – Tulkarm Brigade sun ce jinin mujahidan “ba zai tafi haka nan  ba,” yayin da suke  jawabi ga yahudawa ‘yan mamaya sun jaddada cewa: “Za mu dandana muku kuda, domin mun tanadar muku martani mai zafi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments