Jami’an Sojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Suna Tsoro Bullar Yaki Da Kungiyar Hizbullah

Shugabannin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suna fargabar bullar yaki na har abada don haka suke neman tsagaita wuta a Gaza Duk da matakin zaburar

Shugabannin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suna fargabar bullar yaki na har abada don haka suke neman tsagaita wuta a Gaza

Duk da matakin zaburar da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da fira ministan kasar Benjamin Netanyahu yake yi kan ci gaba da yaki har sai sun kawo karshen kungiyar Hamas gaba daya a Zirin Gaza, sai dai jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito daga jami’an haramtacciyar kasar Isra’ila cewa: Manyan hafsoshin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila suna son ganin a cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza ko da kuwa hakan zai kai ga ci gaba da wanzuwar ‘yan gwagwarmayar kungiyar Hamas a yankin.

Jaridar ta kuma ruwaito jami’an na tabbatar da cewa: Sulhu zai kasance hanya mafi dacewa wajen ganin an sako fursunonin yahudawan sahayoniyya 120 da aka yi garkuwa da su, kamar yadda aka kiyasta yawansu.

Haka nan Jami’an sun kara da cewa: Janar-Janar na haramtacciyar kasar Isra’ila na ganin cewa: Sojojinsu na bukatar lokaci don murmurewa idan har zasu yi yaki da kungiyar Hizbullah ta Lebanon, sannan kuma suna ganin cewa sulhu da Hamas zai iya taimakawa wajen cimma yarjejeniya da kungiyar ta Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments