Qalibaf : Zan Ba Da Fifiko Kan Harkokin Diflomasiyya Idan Aka Zabe Ni

Mohammad Baqer Qalibaf, dan takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 28 ga watan Yuni, ya ce fadada alakar Iran da

Mohammad Baqer Qalibaf, dan takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 28 ga watan Yuni, ya ce fadada alakar Iran da dukkan kasashen duniya na da matukar muhimmanci a gare shi, yana mai jaddada cewa manufofin ketare da diflomasiyya za su kasance “babban ginshikin” gwamnatinsa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Qalibaf, wanda a halin yanzu shi ne kakakin majalisar dokokin Iran, ya bayyana hakan ne a wani shirin gidan talabijin na kasar a ranar Lahadi.

“Na yi imanin cewa batun Iran da matsayin Iran a huldar kasa da kasa na da matukar muhimmanci,” in ji shi, yana mai jaddada cewa diflomasiyya na taka muhimmiyar rawa wajen kara karfin Jamhuriyar Musulunci.

Ya ci gaba da cewa wani muhimmin bangare na al’amuran kasar ya samo asali ne daga ayyukan gwamnati na aiwatar da manufofin kasashen waje.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments