Yemen Zata Ci Gaba Da Samar Da Makaman Drones Da Kuma Amfani Da Su Matukar An Ci Gaba Da Yaki A Gaza

Kakin kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya bayyana cewa kamfanin kera makaman Drone ko jiragen yaki masu konan bakin wake a kasar sun ci gaba

Kakin kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya bayyana cewa kamfanin kera makaman Drone ko jiragen yaki masu konan bakin wake a kasar sun ci gaba da gaggawa, ya kumakara da cewa sojojin kasar Yemen zasu ci gaba da yaki da makiyanta har zuwa lokacinda za’a kawo karshenyaki a Gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Mohammed Abdul-Salam, wanda kuma shi ne shugaban tawagar tattaunawa ta kasar , tanakalto shi yana fadawa tasahr talabijin ta Al-Mayadeen ta kasar lebanin a ranar Alhamis  kan cewa, kasar Yemen ta amfana kuma da yi abinda ake cewa ba zai yu ba, saboda saurin bunkasar kamfanonin kara makaman kasar.

Abdussalam ya kara da cewa kamfanonin kare makaman Drones ya samici gaba mai yawa. Sannan kasar ta sami ci gaba a bangaren kera makamai masu linzami  da kuma fasahar dabarbarun yaki daban daban.

A wani bangaren kakakin kungiyar ta Ansarallah ya bayyana cewa yakin Gaza ya bayyana irin karfin sojen da kasar Yemen take da shi. Sannan ta cimma dukkan manufofinta na shiga yankin tallafawa Gaza.

Abdussalam ya kammala da cewa, kasashen Amurka ta Burtrania sun kasa cimma burinsu na hana kasar kaiwa jiragen HKI ko kuma wadanda sukezuwa HKI masu wucewa da babulmandab kaimasu hare hare.

Kasashen sun kare kare HKI a yakin da take yi da kasar Yemen dangane da Gaza. Gwamnatin kasar Yemen tashiga yaki da HKI ne bayan ta  fara kissan kiyashin da ta ke yi a yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments