‘Yan Takara A Zaben Shugabancin Kasa A Iran Sun Tafkla Muhawara Ta Biyu

‘Yan takara a zaben a zaben shugabancin kasa a Iran, sun fara muhawara ta biyu kai tsaye a gidan talabijin din kasar gabanin zaben da

‘Yan takara a zaben a zaben shugabancin kasa a Iran, sun fara muhawara ta biyu kai tsaye a gidan talabijin din kasar gabanin zaben da za’a gudanar a ranar 28 ga watan watan Yuni.

Muhawarar wacce ita ce karo na biyu a yayin da ya rage mako guda a gudanar da zaben zata mayar da hankali kan tattalin arziki da zamantakewar kasar.

Wannan muhawarar ta biyo bayan wadda aka yi a ranar Litinin, wadda ta ta’allaka kan batun tattalin arziki kawai, wanda ya shafi muhimman batutuwa kamar tsare-tsaren bunkasa tattalin arziki, takunkumi, hauhawar farashin kayayyaki, cinikayyar kasashen waje, da zuba jari.

Yakin neman zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 28 ga wata na ci gaba da gudana, inda ‘yan takara shida ke fafatawa wadanda suka hada da: Mohammad Baqer Qalibaf, Masoud Pezeshkian, Amir-Hossein Ghazizadeh Hashemi, Alireza Zakani, Mostafa Pourmohammadi, da Saeed Jalili.

Zaben dai ya zo ne shekara guda gabanin lokacin da ya kamata a gudanar da shi, sakamakon rasuwar shugaban kasar Mirigayi Shahid Ebrahim Ra’isi da wasu mukarabansa ciki har da ministan harkokin waje Hossien Amir Abdolahian a wani hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a ranar 19 ga watan Mayun da ya gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments